Musa Dattijo Muhammad

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Musa Dattijo Muhammad
Rayuwa
Haihuwa Chanchaga, 27 Oktoba 1953 (70 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta University of Warwick (en) Fassara
Jami'ar Ahmadu Bello
Jami'ar Bayero
Sana'a

Musa Dattijo Muhammad OFR (An haife shi 27 ga Oktoba 1953) masanin shari'a ne na Najeriya kuma Kotun Koli ta Najeriya.[1]

Rayuwar farko[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Musa Dattijo a ranar 27 ga Oktoba 1953 a Chanchaga, karamar hukumar Minna, babban birnin jihar Neja, a arewa ta tsakiyar Najeriya . Ya halarci makarantar Primary School da ke Minna da Sardauna memorial secondary inda ya samu shaidar kammala makarantar sakandare ta yammacin Afirka a shekarar 1971. Ya halarci Jami’ar Bayero da ke Jihar Kano a Arewacin Najeriya inda ya samu takardar shaidar kammala digiri kafin ya wuce Jami’ar Ahmadu Bello inda ya sami digiri na farko a fannin Shari’a a shekarar 1976. Daga baya ya sami digiri na biyu a fannin shari'a daga Jami'ar Warwick a shekarar1983. [2]

Shashin Shari'a[gyara sashe | gyara masomin]

A watan Yulin 2012, an nada shi shugaban kotun kolin Najeriya a matsayin mai shari'a. Ya jagoranci hukuncin kotun koli da ta tabbatar da Gbenga Kaka a matsayin zababben Sanata mai wakiltar Ogun ta Gabas a zaben sanata na 2 ga Afrilu 2011. [3]

Memba na Kungiyoyi[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

Template:Supreme Court of Nigeria

  1. https://www.wikiwand.com/en/Musa_Dattijo_Muhammad
  2. https://www.nairaland.com/4602413/photo-meet-hon-justice-musa
  3. https://www.premiumtimesng.com/tag/musa-dattijo-muhammad